Isa ga babban shafi
Saudiya

Kasashen Turai na bukatar Saudiya ta yi bayani kan Khashoggi

Kasashen Faransa da Birtaniya da Jamus sun bukaci Saudi Arabia da tayi bayani kan bacewar Dan Jarida Jamal Khashoggi, yayin da Saudiyar ta yi barazanar mayar da martini kan duk wata kasa da ta dauki mataki akan ta.

Jamal Khashoggi da ake zargin Saudiya da kashe shi
Jamal Khashoggi da ake zargin Saudiya da kashe shi Middle East Monitor/Handout via REUTERS
Talla

Wannan ya biyo bayan barazanar daukan mataki daga shugaba Donald Trump, yayin da kamfanoni da dama suka janye daga wani taron tattalin arziki da aka shirya gudanarwa a Saudiyar.

Wata sanarwar hadin gwiwa daga Ministocin Harkokin Wajen Birtaniya da Faransa da Jamus na cewa, dole a nemi bahasi daga duk wanda ke da hannu kan bacewar wannan dan jaridan.

Khashoggi, dan jaridan da ke yawan bayyana ra’ayinsa a jaridar Washington Post, ya bace ne bayan ya shiga ofishin jakadancin Saudiyya a birnin Santanbul na Turkiya a  ranar 2 ga watan Oktoba don karbar wasu takardu dangane da aurensa da ke gabatowa.

A ranar Asabar da ta gabata ne, Turkiyya ta ci gaba da matsin lamba ga Saudiya, tana cewa ta ki bada hadin kai a binciken da ake yi na bacewar Khasshogi.

Shugaba Donald Trump ya yi barazanar hukunci mai tsanani kan Saudiya da ta kasance babbar kawar Amurka, sai dai ya ce, hukuncin ba zai shafi  haka ba zai shafi cinikayya tsakaninsu ba musamman ta makamai.

Saudiyya ta ce za ta yi ramuwar gayya a game da duk wani takunkumi ko kuma wani mataki da za a dauka kan kasar game da wannan batu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.