Isa ga babban shafi
Turkiya-Saudiya

Trump ya yi kashedi dangane da bacewar Khashoggi

Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce za a dauki zazzafan mataki a kan Saudiyya matukar dai aka tabbatar da ce kasar da na da hannu a bacewar dan jarida Jamal Khashoggi a lokacin da ya shiga ofishin jakadancin kasar da ke birnin Istanbul na Turkiyya.

Masu zanga-zangar neman sanin makomar Jamal Khashoggi gaban ginin jakadancin Saudiyya Istanbul, 5 ga watan oktoba 2018
Masu zanga-zangar neman sanin makomar Jamal Khashoggi gaban ginin jakadancin Saudiyya Istanbul, 5 ga watan oktoba 2018 REUTERS/Osman Orsal
Talla

Trump, ya bayyana a wata zantawa da tashar talabijin ta CBS da ake shirin watsawa a yau asabar cewa, bisa ga dukkanin alamu mahukuntan Saudiyya na da masaniya dangane da abin da ya faru da dan jaridar, kuma matukar hakan ya tabbatar da za su fuskanci fushin Amurka a cewarsa.

Gidan sarautar Saudiyya na cigaba da musanta zargin cewa yana da masaniya a game da makomar dan jaridar, wanda bayanai ke cewa tun lokacin da ya shiga ofishin jakancin bai fito ba, yayin da wasu bayanan ke cewa ya an hallaki shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.