Isa ga babban shafi
Francophonie

An shiga rana ta biyu a taron kasashe kungiyar francophonie a kasar Armenia

Yau aka shiga rana ta biyu a cigaba da gudanar da taron koli karo na 17 na kungiyar kasashe masu amfani da harshen Faransa a duniya francophonie a birnin Ervan na kasar Armenia, da ya samu halartar shugabannin kasashen duniya cikin su kuwa har da shugaban Faransa Emmanuel Macron.Kungiyar da ke sa ido kan ci gaban harshen Faransaci a duniya ta fitar da rahotonta na shekaru hudu, da ke bayyana harshen a matsayin na 5 a duniya.

Photo shuwagabanin gwamnatoci da kasashen da suka halarci taron kungiyar Francophonie karo na 17 a Erevan Armenia, alhamis 11 octoba 2018.
Photo shuwagabanin gwamnatoci da kasashen da suka halarci taron kungiyar Francophonie karo na 17 a Erevan Armenia, alhamis 11 octoba 2018. ludovic MARIN / AFP
Talla

A shekara ta 2014 an kiyasta cewa, masu amfani da wannan harshe su milyan 274 ne a duniya, to sai dai a halin yanzu adadinsu ya haura milyan 300 a cewar rahoton.

Duk da wannan cigaba da yaren na faransanci ya samu cikin shekaru hudu, hakan na nufin cewa Faransanci na matsayi na biyar ne a duniya baya ga harshen Mandarin, Ingilishi, Spaniyanci da kuma Larabci da ke gabansa.

Rahotan dai na nuni da cewa a halin yanzu kasashen 32 ne ke amfani da Fanransanci a matsayin harshen hukuma, duk da cewa shi ne na hudu da aka fi amfani da shi wajen gudanar da binciken kimiya da sauran hanyoyin sadarwa na zamani.

Yawan masu amfani da harshen na Faransanci a duniya ya samo asali ne sakamakon karuwar jama’a musamman a kasashen Afrika renon Faransa, inda kashi 68% ke zaune a nahiyar a yankin Kudu da Sahara na nahiyar Afrika, sai kuma 22% daga Arewancin nahiyar.

A Congo-Brazzaville ne aka fi amfani da harshe da 59%, Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo a matsayin ta biyu da 50%, sai Côte d’Ivoire d 33%, Sénégal 26%, Mali da Tchad kowanne 17% yayin Niger ke da 13%.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.