Isa ga babban shafi
Saudiya-Turkiya

Amurka na son a yi bincike kan bacewar Khashoggi

Sakataren wajen Amurka Mike Pompeo ya bukaci gwamnatin Saudiyya ta bayar da damar gudanar da bincike domin yaye duhu dangane da makomar dan jaridar kasar mai suna Jamal Khashoggi, wanda ya bata tun lokacin da ya shiga ofishin jakadancin kasar da ke birnin Istanbul na Turkiya.

Jamal Khashoggi ya yi kaurin suna wajen sukar gwamnatin Saudiya
Jamal Khashoggi ya yi kaurin suna wajen sukar gwamnatin Saudiya 路透社
Talla

Jamal, wanda ya shiga ofishin jakadancin domin karbar wasu muhimman takardu a ranar 2 ga wannan wata, rahotanni sun ce an kashe shi a cikin ofishin jakadancin, to sai dai mahukuntan Saudiyya na ci gaba da cewa, ya fice bayan ya karbi wadannan takardu, yayin da mahukuntan Turkiya ke cewa ya kamata Saudiyan ta gabatar da hujjojin da ke tabbatar da cewa dan jaridar ya fice.

Shugaban Turkiya, Recep Tayyip Erdogan ya ce, ofishin jakadancin ba zai iya wanke kansa ta hanyar fadin cewa, dan jaridar ya fice bayan kammala abin da ya kawo sa, don haka ya zama wajibi a gabatar da hujjoji.

Ita ma Turkiya ta bukaci a ba ta dama a hukumance don kutsawa cikin ofishin jakadancin da nufin gudanar da bincike a cikinsa.

Khashoggi ya yi kaurin suna wajen sukar manufofin gwamnatin Saudiya karkashin jarancin yarima Mohammed bin Salman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.