Isa ga babban shafi
Congo

Likitan Congo, Murad sun lashe kyautar Nobel

Kwamitin da ke bada kyautar Nobel ta zaman lafiya mai hedikwata a kasar Norway, ya karrama Denis Mukwege, wani likitan Jamhuriyar Congo saboda taimakon da yake bai wa matan da aka ci zarafinsu, yayin da ita ma Nadia Murad da ke fafutukar yaki da yi wa mata fyade ta samu kyautar ta bana.

Nadia Murad da Denis Mukwege da suka lashe kyautar Nobel
Nadia Murad da Denis Mukwege da suka lashe kyautar Nobel REUTERS/Lucas Jackson/Vincent Kessler
Talla

Mukwege kwararren likita ne a fannin mata da ya shafe shekaru akalla 19 yana tallafa wa matan da suka fuskanci cin zarafi ta hanyar fyade sakamakon yakin basasar da aka dauki tsawon lokaci ana gwabzawa a Jamhuriyar Congo, wanda ya lakume rayukan ‘yan kasar akalla miliyan 6.

A shekarar 1999 Dakta Mukwege, ya gina asibitin da ya sanya wa suna Panzi a birnin Bukavu, da ke gabashin Jamhuriyar Congo, in da daga waccan lokacin zuwa yanzu, likatan da sauran ma’aikatansa suka kula da lafiyar sama da mata dubu 50,000 da aka ci zarafinsu ta hanyar fyade a yakin basasar kasar.

Jamhuriyar Congo ta yi kaurin suna a tsakanin kasashen duniya masu fama da rikici wajen yawaitar cin zarafin mata, hakan ya sa a shekarar 2011, wata mujallar lafiya da ke Amurka, ta bayyana rahoton cewa akalla mata 48 ake yi wa fyade bayan kowace sa’a guda a kasar.

A bangare guda, Nadia Murad 'yar kabilar Yazidi a kasar Iraqi, ta taba fuskantar cin zarafi daga mayakan kungiyar ISIS ta hanyar azabtarwa da fyade, yayin da daga bisani ta zama mai fafutukar yaki da matsalar cin zarafin mata tsakanin al'ummar Yazidi

Berit Reiss-Andersen, shugabar kwamitin bada lambar yabon ta Nobel, ta ce Mukwege da Murad  sun taka muhimmiyar rawa wajen mayar wajen yaki da laifuffukan yaki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.