Isa ga babban shafi
Isra'ila-Palestine

Trump ya goyi bayan kafa kasar Falasdinu

A karon farko shugaba Donald Trump na Amurka ya goyi bayan samar da kasar Isra'ila da kuma kasar Falasdinu daban domin kawo karshen duk wata takaddamar da ake samu.

Shugaban Amurka Donald Trump na jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya
Shugaban Amurka Donald Trump na jawabi a zauren Majalisar Dinkin Duniya 路透社
Talla

Tsarin Majalisar Dinkin Duniya na shekarar 1947 ya tanadi bai wa Isra'ila da Falasdinu ‘yancin cin gashin kai kowacce, yayin da birnin Kudus ya kasance karkashin wata hukuma daban ta kasa da kasa, sai dai shugabannin Larabawa sun ki amincewa da tsarin.

Daga bisani ne aka gabatar da yarjejeniyar Oslo ta shekarar 1990 da ake ganin za ta bai wa Isra'lan da Falasdinawa ‘yancin cin gashin kai, amma wannan yarjejeniya ba ta kai koina ba.

Yanzu haka jagoran Falasdinawa, Mahmud Abba na ci gaba da neman ganin an aiwatar da yarjejeniyar shekara ta 1967 da za ta bai wa Yahudawan Isra'ila kasarsu daban, su ma Falasdinawa tasu daban.

Shi kuwa Firaminstan Isra'ila Benjamin Netanyahu na cewa, karkashin dukkan wata yarjejeniya ala tilas Isra'ila ta karbi harkan tsaron yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.