Deborah Ramirez ta shaida wa New York Times cewa lamarin ya faru ne yayin wani biki a wata makarantar sakadanre a lokacin tana da shekaru 15 yayin da shi kuma Kavanaugh ke da shekaru 17 a duniya.
Sai dai Kavanaugh ya musanta dukkanin zarge-zargen tare da bayyana yunkurin bata masa suna.
Ana bukatar amincewar mambobi 21 na kwamitin Majalisar Dattawa da kuma daukacin ‘yan Majalisar kafin nada Kavanaugh a matsayin alkalin kotun kolin kasar.
Wasu ‘ya’yan jam’iyyar Republican da shugaba Donald Trump sun zargi Ford da wasu ‘ya’yan jam’iyyar Democrat da kokarin haifar da tarnaki wajen tabbatar da Kavanaugh akan wannan mukami.