Isa ga babban shafi
Amurka

Harin bindiga ya hallaka mutane uku a Maryland na kasar Amurka

A Amurka wata ‘yar bindiga ta rasa ranta a dalilin raunin data yiwa kanta a lokacin da ta kai wani hari.Matar ta bude wuta kan mutane da ke ginin wata ma’ajiyar kayayyaki inda ta ke aiki, a gabashin jihar Maryland da ke Amurka, inda ta hallaka mutane uku tare da jikkata wasu uku.

Daya daga cikin yankuna da aka kai harin bindiga a Amurka
Daya daga cikin yankuna da aka kai harin bindiga a Amurka HO / Courtesy of WJXT / AFP
Talla

Jami’an ‘yan sanda na kan aikin tantance hakikanin jinsin maharin ko kuma ‘yar bindigar,inda bincike ya nuna cewa matar ta kaddamar da harin bindigar kan dandazon jama’a, abin da ba a saba gani ba a kasar cewa, mace ta kai irin wannan farmakin.

Shugaban rundunar ‘yan sandan yankin Harford da ke Maryland, Jefferey Gahler ya tabbatar da jikkatar mutane da dama da kuma salwantar rayuka.

Jami’in ya ce, akwai yiwuwar matar ce ta raunata kanta da kanta domin kuwa babu wani dan sanda da ya yi harbi da nufin martani ga harin.

Tuni aka baza jami’an hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI a wurin da harin ya auku.

Ana yawaitar samun hare-haren bindiga kan dandazon al’umma a Amurka, yayin da kundin tsarin mulkin kasar ke kare hakkin mallakar bindigar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.