Isa ga babban shafi
Amurka-Guguwa

Mutane miliyan 1 za su bar gidajensu saboda guguwar Florence a Amurka

Akalla Mutane sama da miliyan daya ne aka bukaci su tsere daga gidajen su sakamakon yadda wata mumunar guguwa mai dauke da ruwan sama da aka yiwa lakabi da Florence ta dumfari Gabashin kasar Amurka.

Trump ya ce ya zanta da shugabancin jihohin da ke fuskantar barazanar guguwar kuma ya tabbatar musu cewa gwamnati a shirye ta ke ta basu dukkanin tallafin da su ke bukata a kowanne lokaci.
Trump ya ce ya zanta da shugabancin jihohin da ke fuskantar barazanar guguwar kuma ya tabbatar musu cewa gwamnati a shirye ta ke ta basu dukkanin tallafin da su ke bukata a kowanne lokaci. Reuters
Talla

Mummunar guguwar wadda ke gudun kilomita 220 cikin sa'a guda ana ganin akwai yiwuwar ta watsu zuwa wasu sassa na kasar, mahukunta suka yi gargadi kan kowa ya kasance cikin shiri.

Shugaba Donald Trump a sakon sa ta twitter ya bayyana guguwar a matsayin daya daga cikin mafi girma, inda ya bukaci Amurka su shirya, su kuma kare kan su.

Shima Gwamnan South Carolina Henry McMaster ya bukaci mutanen gabashin birnin da su bar gidajen su kafin isar iskar ranar alhamis, yayinda aka ba da umurnin rufe makarantu a Yankuna 26 daga 46 da ke Jihar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.