Isa ga babban shafi
Syria

Kasashen duniya na taro kan makomar Idlib na Syria

Shugabannin kasashen Iran da Rasha da kuma Turkiyya na gudanar da taro a birnin Tehran domin fayyace makomar lardin Idlib, wanda shi ne tungar karshe da ta rage a hannun ‘yan bindigar kasar Syria.

Ana fargabar amfani da makami mai guba a farmakin Idlib da gwamnatin Syria ke shirin kaiwa
Ana fargabar amfani da makami mai guba a farmakin Idlib da gwamnatin Syria ke shirin kaiwa Nazeer AL-KHATIB / AFP
Talla

Kafin wannan taro na ranar Jumma'a, Rasha da Syria sun sanar cewa sun shirya tsaf domin kai farmaki da zummar kakkabe ‘yan tawaye daga yankin, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke nuna fargaba dangane da makomar fararen hula.

Hakazalika Turkiyya wadda ke mara wa ‘yan tawayen baya, na fargabar cewa, farmakin zai haifar da kwararar dimbin jama’a zuwa cikin kasar mai makotaka da yankin na Idlib.

A bangare guda, Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinmin Duniya zai gudanar da wani taron gaggawa a ranar Juma’a don tattaunawa game da fargabar amfani da makami mai guba a Idlib bayan Amurka ta ce, tana da bayanan da ke nuna cewa shugaba Bashar al-Assad na shirin amfani da makamin a lardin.

Rundunar sojin Faransa ta ce, za ta yi amfani da karfi a yakin da ake yi a Syria matukar gwamnatin Assad ta yi amfani da makami mai guba kan jama’a.

Babban kwamandan askarawan Faransa Janar Francois Lecointre ne ya yi wannan kashedi, in da ya ce, yanzu haka suna sa ido kan abubuwan da ke faruwa a yankin na Idlib wanda ake kallo a matsayin tungar karshe da ke hannun ‘yan tawayen Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.