Isa ga babban shafi
Amurka

Ban taba tunanin kashe shugaba Assad ba- Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya karyata tattaunawa da ma’aikatar tsaro ta Pentagon kan bukatar kashe takwaransa na Syria, Bashar al-Assad, bayan wani fitaccen dan jarida, Bob Woodward ya fallasa haka a wani sabon littafinsa da ke nuna irin tabargazar da ake tafkawa a fadar White House. Koda dai Fadar ta White House ta bayyana littafin a matsayin mai cike da karerayi.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Leah Millis
Talla

A lokacin da yake magana da manema labarai a ofishinsa da ke fadar White House, shugaba Trump ya ce, ko kadan ba su taba tunanin kashe shugaba Assad ba kamar yadda Woodward ya zarge shi a littafin mai suna Fear : Trump in the White House.

A cikin littafin, Woodward ya ce, Trump ya shaida wa sakataren tsaron kasar, Jim Mattis cewa, yana son a kashe Assad bayan ya kai harin makami mai guba kan fararen hula a cikin watan Afrilun bara.

Littafin ya ce, Mattis ya amsa bukatar Trump amma daga bisani ya gabatar da tsarin takaita hare-haren makami mai guba.

Bayan karyata bayanan da ke kunshe a littafin, shugaba Trump ya kuma ce, yana matukar mamaki kan yadda Majalisar Dokokin Kasar ta ki sauya dokar kazafi.

Shi kan shi Mattis, littafin ya ce, ya taba bayyana Trump a matsayin mutum mai karamar kwakwaluwa, kuma shi ne ya bai wa shugaban shawara kan bukatar girke sojin Amurka a Korea ta Kudu don dakile faruwar yakin duniya na uku.

A cewar littafin, da dama daga cikin makusantan Trump na shan zagi na cin mutunci daga shugaban, amma wasu daga cikinsu kan rama zagin musamman a bayan fage, in da suke bayyana shugaban da tabin hankali da sakarci.

Trump ya ce, littafin wanda za a saki a ranar 11 ga watan nan na Satumba, an buga shi ne don yaudarar Amurkawa a dai dai lokacin da ake shirin gudanar da zaben tsakiyar wa’adi a cikin watan Nuwamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.