Isa ga babban shafi
Syria-Amurka

Trump ya gargadi Syria da kawayenta kan yakin Idlib

Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi gwamnatin Syria da kawayenta, wato Rasha da Iran game da kaddamar da hare-hare kan mai uwa da wabi a lardin Idlib da ke karkashin ikon ‘yan tawaye.

Dakarun Syria na shirin kai hari lardin Idlib
Dakarun Syria na shirin kai hari lardin Idlib GEORGE OURFALIAN / AFP
Talla

A wani sakon Twitter da ya aika, shugaba Trump ya yi gargadin ne don kauce wa gagarumin kuskuren da ka iya sanadiyar mutuwar daruruwan jama’a.

Wannan na zuwa ne bayan rahotannin da ke cewa gwamnatin Syria na shirin kaddamar da gagarumin farmaki kan yankin.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce, kasar za ta mayar da martani kan duk wani harin makami mai guba da gwamnatin Syria ko kawayenta za su iya amfani da shi a Syria.

Ita ma Majalisar Dinkin duniya ta ce, hare-haren ka iya haifar da mummunan sakamakon da zai jefa dubban fararen hula cikin mawuyacin hali.

An dai ci galabar akasarin ‘yan tawayen Syria, yayin da ake ganin farmakin da ake shirin kai wa a Idlib ka iya zama yakin basasa na karshe a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.