Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya na taro kan rikicin Boko Haram a Berlin

Kasashen Najeriya da Jamus da Normay da Majalisar Dinkin Duniya na gudanar da wani taro na musamman a birnin Berlin don tattaunawa kan samar da kudaden sake raya kasashen da rikicin Boko Haram ya yi illa.

Rikicin Boko Haram ya jefa miliyoyin al'umma cikin mawuyacin hali a kasashen yankin tafkin Chadi
Rikicin Boko Haram ya jefa miliyoyin al'umma cikin mawuyacin hali a kasashen yankin tafkin Chadi © AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Taron na kwanaki biyu na daya daga cikin manyan taruka da aka gudanar a bana da zummar raya kasashen yankin tafkin Chadi.

Taron zai mayar da hankali kan samar da tallafin da zai amfanar da jama’a da samar da tsaro ga fararen hula da kuma magance rikice-rikice don maido da zaman lafiya a yankin na tafkin Chadi.

Ana sa ran tara kudaden da yawansu ya kai Dala biliyan 1.56 da za a yi amfani da su wajen biyan bukatun al’ummar yankin da ya hada da arewa maso gabashin Najeriya da Nijar da Chadi da kuma Kamaru da ke fama da hare-haren Boko Haram.

Alkaluma sun nuna cewa, rikicin Boko Haram ya jefa akalla mutane miliyan 10.2 cikin mawuyacin hali a jihohi uku da ke arewa maso gabashin Najeriya kadai.

.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.