Isa ga babban shafi

Sauyin yanayi zai haifar da fari a duniya - Bincike

Masana sun bankado wani sabon bayanai da ke nuna cewar, sauyin yanayin da ake samu a duniya sakamakon dumamar yanayi, zai haifar da yunwa ga kwari da kuma tilasta musu cin kayan abincin da Bil Adama ke nomawa irin su alkama da masara da shinkafa.

Binciken ya nuna cewa sauyin yanayin zai tilastawa kwari cinye abincin da al'umma ke nomawa matakin da zai haifar da gagarumin fari a sassan duniya matukar ba a dauki matakin magancewa ba.
Binciken ya nuna cewa sauyin yanayin zai tilastawa kwari cinye abincin da al'umma ke nomawa matakin da zai haifar da gagarumin fari a sassan duniya matukar ba a dauki matakin magancewa ba. AFP/ PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Jagaoran binciken Scott Merrill daga Jami’ar Vermont, ya ce cin wadannan kayan abinci da suke kashi 42 na abincin da jama’a ke ci a fadin duniya, za su haifar da karancin abinci a duniya da kuma samun rikice rikice.

Binciken ya nuna cewar, dummar yanayin zai haifar da zafin da wadannan kwari zasu gamu da yunwa sosai, abinda zai tilasta musu cin abincin Bil Adama.

Masanan su ne za’a samu yaduwar kwarin a kasashe irin su Faransa da Amurka saboda yanayin da suke da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.