Isa ga babban shafi
WHO-RUWA

Rabin makarantun duniya ba su da tsaftataccen ruwan sha - WHO

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar duniya na fuskantar annoba ganin yadda rabin makarantun da ake da su a duniyar ba su da tsaftacacen ruwan sha da ban daki da kuma kayan wanke hannu.Rahotan Hukumar ya ce akalla yara miliyan 900 ke fuskantar kamuwa da cututtuka daban daban sakamakon wadannan matsaloli.

Rahotan ya ce, matsalar tafi kamari a kasashen da ke Yankin kudu da Sahara da kuma Gabashi da Kudancin Asia.
Rahotan ya ce, matsalar tafi kamari a kasashen da ke Yankin kudu da Sahara da kuma Gabashi da Kudancin Asia. Akintunde Akinleye/Reuters
Talla

Shugaban da ya jagoranci gudanar da bincike da kuma rubuta wannan rahoto, Dr Rick Johnston na Hukumar Lafiya at Majalisar Dinkin Duniyar ya ce babu yadda dalibai za su samu natsuwar daukar darussan karatu a makarantun da basu da tsaftaccacen ruwan sha ko ban daki ko kuma wurin wanke hannaye.

Shugabannin kasashen duniya sun sanya hannu kan kudirin Majalisar Dinkin Duniya na samar da tsaftacacen ruwan sha da kuma ban daki ga kowanne yaro nan da shekarar 2030, amma har yanzu samar da wadannan kayan more rayuwa na fuskantar matsala.

Rahotan wanda UNICEF ta taimaka wajen rubuta shi, ya bayyana cewar kowacce makarantar Firamare da Sakandare daya bisa uku basu da ruwan sha mai tsafta, abinda ya shafi yara miliyan 570, yayin da yara miliyan 620 ba su da makewayi ko ban dakin da za su biya bukatun su.

Rahotan ya ce, matsalar tafi kamari a kasashen da ke Yankin kudu da Sahara da kuma Gabashi da Kudancin Asia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.