Isa ga babban shafi
Faransa- Amurka

Dole Turai ta rage dogaro ga Amurka- Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce, zai gabatar da sabbin kudurori ga Kungiyar Tarayyar Turai don karfafa tsaronta, in da ya ce, dole ne nahiyar ta rage dogaro ga Amurka.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Francois Lenoir
Talla

A yayin gabatar da jawabin sake kaddamar da manufofinsa na diflomasiya a birnin Paris a gaban dimbin jakadun kasar, shugaba Macron ya ce, kasashen Turai ba za su ci gaba da dogaro ga Amurka ba kan sha’anin tsaro, kuma ya rage gare su da su tabbatar da tsaro a yankinsu.

Ana saran kaddamar da kudurorin Macron nan da ‘yan watanni masu zuwa kamar yadda ya shaida wa jakadun 250 da ‘yan majalisa da kuma kwararru kan harkokin huldar kasashen ketare da suka hallara bayan dawowa daga hutun kaka.

Kalaman Macron na zuwa ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya nuna alamomin nesanta kansa daga tsarin kawancen kasashen da ke cikin kungiyar tsaro ta NATO.

Shugaba Trump ya sha diga ayar tambaya kan sahihancin rawar da kasashen Turai ke takawa wajen samar da tsaro a kasashen NATO, yayin da ya yi korafi kan cewa, Amurka na kashe kudade masu yawa kan sojoji don taimaka wa Turai.

A bangare guda, shugaba Macron ya caccaki takwaransa na Syria, Bashar al-Assad tare da gargadin cewa yana dab da haddasa sabon rikicin jefa al’umma cikin mawuyacin hali a lardin Idlib.

Macron ya zargi Assad da kashe mutanensa tare da haifar da gudun hijirar da ya rutsa da dubban al’ummar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.