Paparoma Francois ya ziyarci Ireland don magance matsalar lalata da Yara
Badakalar lalata da yara, bautar da yan mata, da ta mamaye cocin Katolika tun cikin 1980 a Irlande ce makasudin ziyarar aikin kwanaki 2 da shugaban mabiya mazahabar Katolika ta addini Kirista na duniya Paparoma Francois, ya fara a yau assabar a yankin Irland. ziyarar da za ta bashi damar ganawa da wadanda aka ciwa zarafi,A kokarin da yake na kwantar masu da hankali Paparoman ya dau alkawalin ganin an kawo karshen m ummunar labi'ar da limaman cocin ke ta katolika ke aikatawa a kasar ta Irlande.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A yan watanni da suka gabata ma, Paparoman ya amince da murabus din wasu limaman, da suka hada da na kasar Chili, Austaralia da Amruka da aka samu da laifin yin lalata da yara
Ziyarar tasa ta yau assabar a Irland, za ta bashi damar samun tarbe daga dubban mabiya mazahabar ta Katolika, da zasu taru a wani filiin kwallo, na zuwa ne kusan shekaru 40, da wace magabacinsa Jean-Paul II, ya taba kai wa a kasar da mazahabar ta Katolika ke ci gaba da fuskantar koma baya sakamakon abubuwan kunyar da suka dabaibayeta
A marecen yau assabar, Paparomar Francois zai gudanar da adu’oi a cocin St Mary's a gaban kyndran wutar da aka kunna, domin nuna alhini ga wadanda aka ciwa zarafin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu