Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Ali Bouzou mai rajin yaki da bautar da dan adam kan ranar kawo karshen bauta a duniya

Wallafawa ranar:

Yau 23 ga watan agusta ita ce ranar da MDD ta kebe domin tunawa da shelanta kawo karshen bauta a duniya, matakin da ya biyo wani bore da aka gudanar a rana makamanciyar ta yau a shekara ta 1791 a Santa Domingo, wadanda a yau ake kira Haiti da kuma Jamhuriyar Dominican.To sai dai duk da cewa a shekarun da suka biyo baya a samar da dokokin da ke haramta bautar da dan adam a sassan duniya, har yanzu a wasu kasashe na Afirka ana tafiyar da wannan mummunar dabi’a ta wata fuska.Ali Bouzou, shi ne sakataren kungiyar Timidria da ke yaki da bautar da dan adam a jamhuriyar Nijar, ya ce tabbas har yanzu akwai inda ake bautar da jama’a a kasar tamkar dai lokacin jahiliyaya.

Majalisar Dinkin Duniya ta ware kowace ranar 23 ga watan Agusta domin bikin tunawa da shelanta kawo karshen bauta a duniya.
Majalisar Dinkin Duniya ta ware kowace ranar 23 ga watan Agusta domin bikin tunawa da shelanta kawo karshen bauta a duniya. YouTube
Sauran kashi-kashi
  • 03:16
  • 03:19
  • 03:26
  • 03:17
  • 03:40
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.