Isa ga babban shafi
Brazil

Brazil ta fara kwashe 'yan gudun hijirar Venezuela daga kan iyakarta

Gwamnatin Brazil za ta kwashe ‘yan kasar Venezuela sama da dubu daya daga garin Roraima kusa da iyakar kasashen biyu, domin rarraba su a sauran garuruwa na kasar ta Brazil bayan da tarzoma ta barke tsakanin bakin haure da aal’ummar yankin.

yan gudun hijirar Venezuela na tura akwatunansu daga  Rumichaca, dake kan iyakar kasar da Brazil   18 août 2018.
yan gudun hijirar Venezuela na tura akwatunansu daga Rumichaca, dake kan iyakar kasar da Brazil 18 août 2018. REUTERS/Luisa Gonzalez/File Photo
Talla

Dubban mutane ne ke ci gaba da kwarar zuwa Brazil da Venezuela da kuma Colombia, sakamakon matsalar tattalin arziki da Venezuela ke fama da ita.

Wata wakiliyar gwamnati Viviane Asse, ta sanar da manema labarai a garin Boa Vista babban birnin yankin Amazoniya cewa, matakin sake rarraba yan gudun hijirar na Venezuela a cikin kasar ta Brazil, zai fara ne a karshen wannan wata na Ogusta da muke ciki, sai dai ba ta bayyana garuruwan da za a kai su ba

Uwargida Esse dai, na da ga cikin yan komitin ministoci da a ranar talatar da ta gabata suka ziyarci yankin kan iyakar Paracaima, inda a ranar assabar da ta gabata aka samu tashin hankali tsakanin al’umar yankin, da kuma yan gudun hijirar kasar ta Venezuela.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.