Iran zata gabatar da wani jirgin saman yaki da ta kera
Kasar Iran ta sanar da cewa cikin wannan mako da za ta kaddamar da wani jirgin sama na yaki mai muhimmanci, sannan kuma zata bada karfi wajen kera makamanta masu linzami.
Wallafawa ranar:
Ministan tsaro na kasar Brig. Janar Amir Hatami ne ya sanar da haka inda yake cewa, a ranar Laraba 21 ga watan ogusta ne da kasar za ta yi bukin ranar masanaantun da zaayi ne za’a gabatar da jirgin yakin.
Shugaba Donald Trump na Amurka dake adawa da dukkan matakan kara karfin da Iran ke yi , a watan 5 daya gabata ya janye Amurka daga cikin yarjejeniyar Nukliyar da manyan kasashen duniya suka kuklla da Iran a shekara ta 2015 don sassauta mata takunkumi .
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu