Isa ga babban shafi
Falasdinu

Guterres ya gabatar da kudurori 4 na kare rayukan Falasdinawa

Sakatare janar na majalisar dinkin duniya Antonio Guterres, ya gabatar da wasu kudurori 4 da za a yi amfani da su wajen baiwa Falasdinawa kariya daga cin zarafin da Isra’ila ke musu.

Wani Bafalasdine mai fama da nakasa yayin jifan sojojin Isra'ila da duwatsu, a lokacin da dubban Falasdinawa ke zanga-zanga a yankin Gaza, inda suke neman Isra'ila ta maida musu yankunan da ta mamaye. 17 ga Agusta, 2018.
Wani Bafalasdine mai fama da nakasa yayin jifan sojojin Isra'ila da duwatsu, a lokacin da dubban Falasdinawa ke zanga-zanga a yankin Gaza, inda suke neman Isra'ila ta maida musu yankunan da ta mamaye. 17 ga Agusta, 2018. REUTERS/Mohammed Salem
Talla

Kudurorin na kunshe ne a cikin rahoton da zauren majalisar dinkin duniya ya bukata, domin daukar matakin kawo karshen sabon rikicin da ya barke tsakanin Isra’ila da falasdinawa a yankin Gaza, inda daga watan Maris zuwa yanzu, sojin na Isra’ila suka hallaka Falasdinawa 171.

Kudurorin da babban sakatare Guterres ya gabatar sun hada da, tura dakarun majalisar dinkin duniya, domin baiwa fararen hular Falasdinawa kariya daga sojin Isra’ila, da kuma neman amincewar kwamitin tsaron majalisar, wajen samar da wannan runduna ta musamman.

Sauran kudurorin sun hada da kafa tawagar sa ido kan shingayen binciken ababen hawa da sauran wuraren da Isra’ila ta mamaye, domin bada rahoton cin zarafin Falasdinawa a duk lokacin da hakan ta faru, sai kuma kara yawan tallafin da ake baiwa yankin Falasdinawa domin inganta jin dadin rayuwarsu.

Sakataren majalisar dinkin duniya Guterres ya ce ba shakka bin hanyar diflomasiya wajen warware rikicin Isra’ila da Falasdinawa shi ne mafi dacewa, sai dai tilas ne majalisar ta yi amfani da karfin soja idan hakan ya zama dole, wajen kare rayuka da dukiyar Falasdinawa fararen hula daga sojin Isra’ila.

Ko a ranar Juma’ar nan da ta gabata, sojin Isra’ila sun harbe wasu Falasdinawa biyu har lahira, wadanda ke cikin masu zanga-zanga a kan iyakar yankin Gaza da kasar ta Isra’ila, inda sojin kasar suka jikkata karin wasu Falasdinawan akalla 270.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.