Isa ga babban shafi
India-Africa

Tsutsotsin gona sun yi kaura zuwa India daga Afrika

Wasu masana daga Majalisar Dinkin Duniya sun bayyana cewar wasu tsutsotsi da ke yi wa amfanin gona matukar illa da aka samu a Afrika da ake kira armyworms, yanzu haka sun isa India, yayin da suke barazana ga miliyoyin manoman da ke fadin nahiyar Asia.

Tsutsar ta fi yin illa ga gonar masara
Tsutsar ta fi yin illa ga gonar masara Riccardo Gangale/Bloomberg via Getty Images
Talla

Masanan sun ce wadannan tsutsotsi da ke tafiya a cikin bataliya sun fi bukatar gonakin masara, kuma su kan ci amfanin gona sama da kashi 80 da suka hada da shinkafa da kayan marmari da gyada da kuma auduga.

Kundhavi Kadiresan, jami’in Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, ya ce tsutsotsin za su yi matukar illa ga tarin manoman masara da shinkafa sosai, duk da yake ba za su iya bada adadin mutanen da abin zai shafa ba.

Ita dai wannan tsutsa in ji masanan, na iya tafiyar kilomita 100 ta sama a cikin dare, kuma mata daga cikinsu na iya saka kwai har 1,000 a rayuwarsu.

Cibiyar Binciken Ayyukan Noma da ke India ta yi shelar gargadi ga manoman kasar bayan gano tarin tsutsotsin a Jihar Karnataka, yayin da kafofin yada labaran India ke cewa tsutsar na yaduwa sosai.

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, rabin kasashen da ke yammacin sahara sun gabatar da rahoto na samun tsutsar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.