Yaran da Saudiya ta kashe a Yemen sun kai 40
Kungiyar Agaji ta Red Cross ta ce, kananan yara 40 aka kashe a wani hari da rundunar hadaka da Saudiya ke jagoranta ta kai kan wata motar safa a arewacin Yemen, alkaluman da suka ninka wadanda kungiyar ta fitar a baya.
Wallafawa ranar:
Fitar da sabbin alkaluman na zuwa ne bayan gudanar da jana’izar kananan yaran 'yan makaranta a ranar Litinin a makabartar lardin Saada da ke karkashin ikon 'yan tawayen Houthi.
Dubban ‘yan kasar Yemen sun nuna bacin ransu kan Saudiya da Amurka a yayin gudanar da jana’izar yaran.
Mahalarta jana’izar sun yi ta daga hotunan yaran da aka kashe da kuma furta munanan kalamai kan Saudiya da Amurka.
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci gudanar da sahishin bincike kan kazamin harin na ranar Alhamis.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu