Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falasdinawa

Netanyahu ya bukaci tsagaita wuta tsakaninsa da Hamas

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bukaci tsagaita wuta daga Sojin Hamas a wani jawabi karon farko da ya yi game da rikicin baya-bayan nan da ke tsakanin Isra’ilan da Gaza wanda ke ci gaba da haddasa asarar rayuka.

A cewar Netanyahu ba su da burin da ya wuce yakar 'yan ta'addan na yankin Gaza da ke barazana ga tsaronsu.
A cewar Netanyahu ba su da burin da ya wuce yakar 'yan ta'addan na yankin Gaza da ke barazana ga tsaronsu. REUTERS/Ronen Zvulun
Talla

Kasar Masar da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya ne ke shiga tsakanin don tabbatar da zaman lafiya a rikicin baya-bayan nan tun daga watan Yuli tsakanin bangarorin biyu wanda kuma sai a wannan karon ne Isra’ilan ta tsoma baki don tsagaita rikicin.

A jawabin da ya gabatar yayin zaman majalisar kasar Netanyahu, ya ce basu da fatan daya wuce ganin bayan ‘yan ta’addan da ke yankin na Gaza, ban da hakan ba bu abin da suke bukata, amma dai suna kira ga tsagaita wuta.

Akalla Falasdinawa 168 Isra’ila ta hallaka tun bayan barkewar sabon rikicin kan iyaka a ranar 30 ga watan Maris din da ya gabata, amma sojin Isra’ila daya ne kadai Hamas ta hallaka kawo yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.