NASA ta yi nasarar harba kumbon da zai kusanci Rana
Hukumar binciken sararin samaniya ta Amurka NASA ta samu nasarar harba kumbonta da ta sanyawa suna ‘Parker Solar Probe’ wanda ake sa ran zai zama na farko da zai kusanci rana domin gudanar da bincike kanta.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kumbon dai ya tashi ne daga cibiyar hukumar ta NASA ta Cape Canaveral da ke jihar Florida.
A ranar Asabar 11 ga watan Agusta, 2018, NASA ta shirya harba kumbon amma ta dage zuwa yau ranar Lahadi, sakamakon fuskantar tangardar na’ura .
Kumbon na Parker Solar Probe da aka gina kan dala biliyan daya da rabi ana sa ran idan zai shafe shekaru akalla 7 kafin ya isa kusa da Rana don soma bincike, kan wasu daga cikin al’amuran da ke tattare da ita, musamman yanayin kakkarfar guguwa da ke zagaya ciki da wajenta cikin tsakanain gudu.
Masana suna sa ran kumbon na ‘Parker Solar probe’ zai taimaka musu wajen hasashen lokacin da kakkarfar guguwar daga ran aka iya ketowa doron duniya.
Kumbon dai zai rika tsala tsananin gudu ne bisa saurin tafiyar da za ta zarta kilomita dubu 400,000 a sa’a guda, idan kuma ya kusanci Ranar, ana sa ran gudun zai karu zuwa kilomita dubu 700,000 a sa’a daya.
Kumbon dai gina shi da kaurin inchi hudu da rabi, da zai bashi kariya daga karfin zafin rana mafi tsanani da ake ji a doron duniya da ya ninka sau 500, wato kwankwacin zafin digiri 1, 371 a ma’aunin Celcsius.
Sai dai wasu na ganin abu ne mayuwaci hakar masanan ta cimma ruwa la’akari da cewa masana sun dade da yin hasashen cewa zafin tsakiyar rana ka iya zarta digiri miliyan 15 a ma’aunin yanayi na Celsius.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu