Ma'aikacin tashar jirgin sama ya sace jirgi a Amurka
Wani ma’aikacin jirgin sama a Amurka ya sace tare da tashi da wani jirgin Fasinja daga tashar Seattle-Tacoma kafin daga bisani ya fado kasa ya mutu.
Wallafawa ranar:
Hukumomin tashar, sun tabbatar da cewa matashin mai shekaru 29 ya tashi da jirgin ne ba tare da masaniyar kowa ba, matakin da ya sa wani karamin jirgin jami’an tsaro ya bi bayansa amma kuma ya gaza sakko da jirgin.
Rahotanni sun ce da misalin karfe 8 na daren jiya ne matashin wanda kamfanin bai bayyana sunansa ba ya tashi da jirgin mai daukar mutane 76 amma saboda rashin kwarewa jirgin ya fado a dai dai tsibirin Ketron ko da dai jami’an filin jirgin saman sun yi ta bashi Umarnin yadda zai saukar da jirgin don tserar da rayuwarsa.
Hukumar gudanarwar filin jirgin saman ta ce matashin na daga cikin hadiman jirgi da ke aikin kula da shi bayan dawowa daga tafiya dama yayin tafiya haka zalika yana daga cikin masu bayar da umarnin tashin jirgin.
Tuni dai hukumar tsaron Amurka ta FBI ta ce abin da matashin ya aikata ba ta’addanci ba ne face karambani haka kuma ta sha alwashin kara matakan tsaro a filin jirgin wanda ta ce rashin matakan tsaron ne ya haddasa lamarin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu