Isa ga babban shafi
Iran-Amurka

Iran ta nanata kudirinta na kin tattaunawa da Amurka

Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif ya ce babu wani shirin ganawa tsakaninshi da takwarinshi na Amurka Mike Pompeo ko ma duk wani Jami’I na Iran da Amurka yayin babban taron Majalisar Dinkin Duniya da ke kusantowa.

Ministan harkokin wajen Iran Mohammed Javad Zarif.
Ministan harkokin wajen Iran Mohammed Javad Zarif. مهر
Talla

Yayin zantawarsa da Kamfanin dillacin labarai na Tasnim Zarif ya nanata matsayar kasar na cewa babu batun wata tattaunawa yayin taron haka zalika sun yi watsi da duk wani tayin Amurka kan tattaunawa da Iran ba.

Ko a Litinin din da ta gabata shugaba Hassan Rouhani ya yi fatali da bukatar Donald Trump na Amurka ta ganawa da shi inda ya gindaya sharadin cewa har sai ya koma cikin yarjejeniyar nukiliyar kasar ta 2015 da ta cimma da kasashen duniya, matakin da ake ganin yana da nasaba da sabbin takunkuman da Amurkan ta mayar kan Iran.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.