Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako, wanda ya saba tattaunawa da kuma bitar manyan al'amuran da suka faru a cikin mako, ya soma ne da waiwayen halin da alakar Amurka da Iran ke ciki, bayan da shugaba Donald Trump ya bayyana cewa a shirye yake ya tattauna da gwamnatin Iran domin cimma sabuwar yarjejeniya kan nukiliyarta.
Sauran kashi-kashi
-
Muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya gabata
Masu sauraro daga sashin Hausa na RFI cikin shirin Mu Zagaya Duniya da saba zabo wasu daga cikin muhimman labarun lamurran da suka wakana a makon da ya gabata, domin bitarsu.A ranar Larabar da ta gabata al'ummar Musulmin Najeriya suka bi sahun takwarorinsu na duniya wajen gudanar da Sallar Idi Karama, wadda aka saba gudanarwa bayan kammala azumin watan Ramadan.13/04/202420:01 -
Karin kudin wutar lantarki ya fusata 'yan Najeriya
Shirin Mu zagaya duniya na wannan mako ya duba batun karin kudin wutar lantarki a Najeriya, halin da ake ciki a Gabas ta tsakiya da kuma rikicin siyasar Togo.06/04/202419:40 -
Bitar labaran mako: Yadda aka ceto daliban Kuriga a Kadunan Najeriya
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan mako tare da Rukayya Abba Kabara ya yi bitan wasu daga cikin labaran da suka fi daukar hankali a makon da ya wuce ciki har da labarin yadda gwamnatin Najeriya ta ceto daliban Kuriga da ke Jihar Kaduna tare da sada su da iyalan su.30/03/202419:30 -
Dubi akan matakin gwamnatin mulkin sojin Nijar na katse huldar aiki da dakarun Amurka
Daga cikin muhimman batutuwan da shirin ya waiwaya a wannan makon akwai matakin Gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar na kawo karshen yarjejeniyar tsaro da ke tsakanin kasar da Amurka.23/03/202419:13 -
Matakin Najeriya na bude iyakokin da ta rufe tsakaninta da Jamhutiyar Nijar
Daga cikin labarun da shirin ya kunsa a wannan makon, akwai matakin da Najeriya ta dauka na bude iyakokin da ta rufe tsakaninta da Jamhutiyar Nijar, tare da janye baki dayan takunkuman da ta kakaba mata.Gwamnatin Birtaniya ta ce a shirye take ta baiwa ‘yan dubban ‘yan Rwanda da ke neman mafaka fam dubu uku kowannensu, to amma fa a bisa sharadin za su amince a mayar da su gida daga kasar ta Birtaniya16/03/202419:19