Isa ga babban shafi
Rasha-Iran

Rasha ta yi tir da takunkuman Amurka kan Iran

Kasar Rasha ta bayyana takaicin ta da yadda Amurka ta yi gaban kan ta wajen dorawa Iran sabbin takunkumai.Kalaman na Rasha na zuwa a dai dai lokacin da Amurkan ke ikirarin katse harkokin kasuwancin da ke tsakaninta da kowacce kasar da ta ci gaba da kasuwanci da Iran.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. REUTERS/Sergei Karpukhin
Talla

Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta ce Rasha za tayi iya bakin kokarin ta wajen ganin ta ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka kulla a shekarar 2015.

Tuni dai wasu kasashe da kamfanoni suka fara tsorata da matakin takunkuman na Amurka, ciki kuwa har da katafaren kamfanin Jamus Daimler wanda ke tsaka da wani aiki da kamfanonin Iran din.

Shugaba Donald Trump na Amurka dai ya gargadi kasashen duniya game da hadarin da ke tattare da ci gaba da kasuwancin da Iran inda ya ke akwai yiwuwar takunkuman su shafi kasashe da kamfanoni da suka yi kunnen kashi wajen kin katse kasuwanci da Iran.

Sai dai tuni kungiyar kasashen Turai ta hannu Federico Mogherini ta yi watsi da takunkumin na Amurka, inda ta bukaci kamfanonin da ke Yankin da su cigaba da huldar su da Iran.

Matakin takunkuman na Amurka kan Iran wanda ta raba shi gida biyu ta kuma sanar da kashin farko a jiya Talata wanda kai tsaye ya shafi alakarta da kasashe ta fuskar musayar kudade ko kuma kasuwancin da ke tsakaninsu.

Kashi na biyu na takunkuman wanda zai fara aiki a ranar 5 ga watan Nuwamba, shi kuma kai tsaye zai shafi albarkatun man fetur da Iran ke siyarwa kasashen duniya, inda Amurkan ta gargadi kasashe irinsu China India da kuma Turkiyya kan su kauracewa sayen man daga Iran, ko da dai dukkaninsu suna kokarin bijirewa umarnin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.