Trump ya gargadi masu hulda da Iran
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kakkausan gargadi kan duk wanda ya ci gaba da huldar kasuwanci da Iran bayan takunkuman da ya sake kakaba wa kasar.
Wallafawa ranar:
A wani sakon Twitter da ya fitar, shugaba Trump ya ce, “duk wanda ke huldar kasuwanci da Iran, ba zai ci gaba da huldar kasuwanci da Amurka ba.”
A cikin daren da ya gabata ne, wasu daga cikin takunkuman da Amurka ta kara lafta wa Iran suka fara aiki, yayin da takunkumai masu tsauri da suka shafi fitar da man fetir za su fara aiki a cikin watan Nuwamba mai zuwa.
Shugaban Iran Hassan Rouhani ya bayyana matakin Trump a matsayin “yakin karya lagwan abokin hamayya” da zimmar dasa kiyayya tsakanin Iraniyawa.
Kungiyar Tarayyar Turai ta soki matakin dawo da takunkuman, in da ta lashi takobin kare kamfanonin da ke halastacciyar harkar kasuwanci da Iran.
Takunkuman na zuwa ne bayan Amurka ta janye daga yarjejeniyar nukiliyar da Iran ta cimma da manyan kasashen duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu