Isa ga babban shafi
EU-Iran

EU za ta bijirewa bukatar Amurka kan yanke hulda da Iran

Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi kasashen duniya game da ci gaba da kasuwanci da Iran bayan matakan da ya dauka na dawo mata da takunkuman da Amurkan ta sassauta mata a baya.Sai dai matakin na zuwa a dai dai lokacin da kungiyar EU ke kara jaddada matsayarta kan kare manufofin kasuwancinsu a kasar ta Iran.

Federica Moghereni ta ce zabi ya ragewa kasashen su zabi wadda za su yi kasuwanci da ita, amma batun alakarsu da Iran za ta dore kamar yadda suka faro.
Federica Moghereni ta ce zabi ya ragewa kasashen su zabi wadda za su yi kasuwanci da ita, amma batun alakarsu da Iran za ta dore kamar yadda suka faro. رویترز
Talla

A wani sako da Trump ya wallafa da sanyin safiyar yau Talata, ya ce takunkuman karya tattalin arziki kan Iran suna nan daram ba sassauci haka zalika dole ne kowacce kasa ta zabi ko dai kasuwanci da Amurka ko kuma kasuwanci da Iran.

Tuni dai wasu kamfanoni da kasashe suka fara razana da matakin na Amurka ciki har da katafaren kamfanin kera-keran manyan motoci na Jamus Daimler, wanda ya fitar da sanarwar katse duk wata harkar cinikayya tsakaninsa da kasar ta Iran.

Sai dai Kungiyar Tarayyar Turai EU, ta bakin shugabar hukumar kare manufofinta a kasashen duniya Federica Moghereni ta ce suna nan kan bakarsu na ci gaba da kasuwancin da ke tsakaninsu da Iran.

Tuni dai kasuwanni a Iran suka fara fuskantar matsaloli duk kuwa da matakin da gwamnati shugaba Hassan Rouhani ta dauka na janye wasu dokokin musayar kudaden ketare baya ga cire haraji kan duk masu shigo Gold da kuma takardun kudin kasashen ketare.

Ana ganin dai takunkumin Amurkan nag aba a cikin wata Nuwamba da zai shafi kasashen da ke sayen man ta irinsu China India da kuma Turkiyya zai fi yi mata illa ko da kuwa sun yi watsi da bukatar ta Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.