Isa ga babban shafi
Indonesia

Girgizar kasa ta hallaka mutane kusan 100 a Indonesia

Masu aikin agaji na ci gaba da neman wadanda suka tsira da rayukansu a wata mummunar girgizar kasa da ta afka wa kasar Indonesia, in da ta lakume rayukan mutane kusan 100.

Wani mazaunin yankin da girgizar kasar ta afku yana kai-kawo kan buraguzan gine-gine a Lombok
Wani mazaunin yankin da girgizar kasar ta afku yana kai-kawo kan buraguzan gine-gine a Lombok Reuters/路透社
Talla

Masu aikin agajin na binciken buraguzan gine-ginen da suka rushe da suka hada da gidajen da Masalattai da makarantun, yayin da buraguzan suka binne mutane da dama da ransu.

Mai magana da yawun Hukumar Agajin Gaggawa ta kasar, Sutopo Purwo Nugroho ya ce, suna kyautata zaton karuwar adadin mutanen da suka mutu, ganin irin ta'adin da girgizar ta haifar.

Tuni girgizar kasar ta haifar da fargabar samun ambaliyar ruwa ta  tsanami duk da cewa daga bisani wannan fargaba ta kau.

Hukumomi sun ce, girgizar kasar ta katse wutar lantarki a daukacin tsibirin Lombok, yayin da ake ci gaba da kula da daruruwan mutanen da suka samu rauni a filin Allah ta Ta'ala da kuma tantunan da aka kafa saboda tsoron shiga cikin gine-gine.

Najmul Akhyar, shugaban yankin Lombok ya ce, kashi 80 na gidaje da makarantu da asibitocin yankin sun lalace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.