Isa ga babban shafi
Afghanistan

Akalla mutane 30 ne suka mutu a Afghanistan

Wasu tagwayen hare hare da aka kai wani masallacin mabiya Shi’a a Afghanistan ya yi sanadiyar mutuwar mutane akala 29 da kuma raunata wasu 81,wadanan hare-hare sun kada zukatan kungiyoyin kasar da na waje.

Masallacin da yan ta'ada suka kaiwa hari a Afghanistan
Masallacin da yan ta'ada suka kaiwa hari a Afghanistan FARID ZAHIR / AFP
Talla

Kungiyar Taliban ta nisanta kan ta daga wannan hari, da ake zaton yan kungiyar Isil ne suka aikata shi.

Maharan saye da niqab sun kutsa cikin masallacin kafin daga bisali su tayar da jigidar bama-bamai da suke dauke da su.

Masu bincike za su mayar da hankali zuwa wasu hanyoyin da yan ta’ada ke amfani da su domin gano kungiyar dake da alhakin wannan hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.