Isa ga babban shafi
Yemen

Tanttance hanyoyin kawo karshen rikicin Yemen

Majalisar Dinkin Duniya tace zata shirya wani taron sasanta rikicin kasar Yemen ranar 6 ga watan Satumba a Geneva, domin tsara hanyoyin da za’a bi wajen cimma zaman lafiya a kasar.

Taswiwar kasar Yemen
Taswiwar kasar Yemen DR
Talla

Jakadan Majalisar, Martin Griffiths ya shaidawa kwamitin sulhu cewar, akwai hanyar warware rikicin kasar ta hanyar tattaunawa, inda ya bukaci manyan kasashen duniya da su goyi bayan shirin.

Griffiths yace tattaunawar zata bude kofar musayar ra’ayi da kuma kulla yarjejeniya tsakanin bangarorin da basa ga maciji da juna.

Akalla mutane kusan 10,000 aka kashe a rikicin kasar cikin su harda tsohon shugaban kasa Ali Abdallah Saleh.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.