Isa ga babban shafi

FAO na neman dala miliyan 120 don tallafawa wadanda suka tagayyara

Hukumar kula da ayyukan noma ta Majalisar Dinkin Duniya FAO, ta kaddamar da gidauniyar Dala miliyan 120, domin taimakawa kasashen Afghanistan, Syria, Sudan da kuma wasu kasashen da duniya ta manta da halin da suke ciki.

Wasu 'yan kasar Sudan ta Kudu da tashin hankali ya raba da muhallansu, a sansanin 'yan gudun hijira da ke yankin Arua District, a arewacin kasar Uganda. 12 ga watan Agusta, 2017.
Wasu 'yan kasar Sudan ta Kudu da tashin hankali ya raba da muhallansu, a sansanin 'yan gudun hijira da ke yankin Arua District, a arewacin kasar Uganda. 12 ga watan Agusta, 2017. REUTERS/Jason Patinkin
Talla

Hukumar Majalisar Dinkin Duniyar tace rashin samun agajin gaggawa zai jefa rayuwar miliyoyin mutanen da tuni suka tagayyara a wadannan kasashe cikin mummunar yanayi nan da watanni shida masu zuwa, sakamakon yunwa da mummunan yanayi.

Hukumar ta FAO, dake fama da karancin kudaden aiki ta bayyana kasashen dake fama da matsalolin fari da tashin hankalin dake hana jama’ar su noma abinda zasu ci da suka hada da Afghanistan da Sudan da Syria da Bangladesh da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, yayin da kasashe irin su Haiti da Iraqi da Myanmar da Yankin Sahel ke fuskantar ambaliya.

Sanarwar hukumar yace, wadannan dalilai ya sa take bukatar dala miliyan 120 cikin gaggawa domin kai dauki ga mutane sama da miliyan 3 da rabi a cikin watanni 6 masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.