Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Dr Abbati Bako kan matakin Iran na kin tattaunawa da Amurka

Wallafawa ranar:

Kasar Iran ta ce ba za ta shiga shirin tattaunawa da kasar Amurka ba har sai ta koma cikin yarjejeniyar nukiliyar da aka kulla da ita a shekarar 2015.Mai bai wa shugaba Hassan Rouhani shawara, Hamid Aboutalebi ya ce mutunta kasar da rage tankiyar da ake samu tsakanin kasar da Amurka da komawa cikin yarjejeniyar nukiliyar da aka kulla ne kawai za su bude kofar tattaunawa a tsakanin su.Jami’in ya ce babu yadda za su tattauna da wanda ke karan tsaye kan dokokin duniya da barazanar murkushe kasashe da kuma sauya matsayi a ko da yaushe.Nura Ado Suleiman ya tattauna da Dr Abbati Bako, masanin siyasar duniya kuam ga yadda zantawar su ta gudana.

An ci gaba da fuskantar musayar yawu tsakanin Amurka da Iran ne tun bayan ficewar Donald Trump daga yarjejeniyar Nukiliyarta a baya-bayan nan.
An ci gaba da fuskantar musayar yawu tsakanin Amurka da Iran ne tun bayan ficewar Donald Trump daga yarjejeniyar Nukiliyarta a baya-bayan nan. scroll.in
Sauran kashi-kashi
  • 03:16
  • 03:19
  • 03:26
  • 03:17
  • 03:40
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.