'Yan ci rani fiye da 1,500 sun hallaka a kokarin isa Turai - MDD
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, IOM ta ce sama da ‘yan ci rani 1,500 ne suka rasa rayukansu, a shekarar 2018 da muke ciki, yayinda sukai kokarin ketare tekun Mediterranean, domin isa nahiyar turai.
Wallafawa ranar:
Hukumar ta IOM ta ce karo na biyar kenan da ake samun adadin ‘yan ci ranin da suka hallaka cikin shekaru biyar a jere.
Rahoton ya kara da cewa ‘yan ci rani, dubu 1,111 sun hallaka ne yayin kokarin ketara teku daga Libya zuwa Italiya, 304 kuma sun salwanta ne a kokarin isa kasar Spain, sai kuma ‘yan ci ranin 89 da suka nutse a teku, yayin kokarin isa kasar Girka.
Wata kididdiga a baya bayan nan, ta nuna cewa ‘yan ci rani dubu 55, 000 ne suka kwarara zuwa nahiyar turai daga watan Janairu zuwa Yuli na 2018, alkalumman da ke nuna an samu raguwar, kashi 50 na yawan wadanda suka ketara teku zuwa nahiyar turan a shekarar 2017.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu