Isa ga babban shafi
Amurka- 'yan cirani

Wa'adin kotu kan hada yaran 'yan cirani da iyayensu ya kare

Yau alhamis, 26 ga watan Yunin 2018, ita ce ranar karshe da wata kotu ta bai wa gwamnatin Amurka domin sake hade yara sama da dubu biyu da aka raba da iyayensu tun cikin watan mayun da ya gabata, bayan da tsallaka iyakar kasar daga Mexico.

Tun a jiya laraba jajibirin karewar wa’adin da kotu ta bai wa gwmanati domin sake hade iyalan, gwamnatin Amurka ta fara aikin neman wasu daga cikin iyayen domin danka masu ‘yayansu.
Tun a jiya laraba jajibirin karewar wa’adin da kotu ta bai wa gwmanati domin sake hade iyalan, gwamnatin Amurka ta fara aikin neman wasu daga cikin iyayen domin danka masu ‘yayansu. © RFI / Anne Corpet
Talla

Tun lokacin da shugaba Donald Trump ya bayar da umurnin raba kananan yaran da iyayensu sakamakon shiga kasar ta Amurka ba a kan ka’ida ba, matakin ke fuskantar mummunar suka a ciki da kuma wajen kasar ta Amurka.

Bayan fitar da wani faifai mai dauke da muryoyin kananan yara da aka raba da iyayensu na kwala ihu a wata cibiya da aka tattara su, wasu jihohi na kasar suka nuna bijirewarsu a game da matakin, yayin da wasu suka shigar da kara a gaban kotu domin kawo karshen hakan.

Tun a jiya laraba jajibirin karewar wa’adin da kotu ta bai wa gwmanati domin sake hade iyalan, gwamnatin Amurka ta fara aikin neman wasu daga cikin iyayen domin danka masu ‘yayansu.

A jimilce dai kananan yara 2,551 ne da shekarunsu suka kama daga 5 zuwa 17 aka kwace daga hannun iyayensu, inda aka tsare su a wasu cibiyoyi na musamman saboda sun shiga Amurka ba da izini ba a cewar gwamnatin Trump.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.