Isa ga babban shafi

Takunkumai za su ci gaba da aiki kan Korea ta Arewa - Amurka

Amurka ta bukaci kasashen China da Rasha, da kuma sauran kasashen duniya, su ci gaba da mutunta takunkuman karya tattalin arzikin da aka kakabawa Korea ta Arewa, har sai kasar ta cika alkawarin da ta dauka, na lalata ilahirin makaman nukiliyar da ta mallaka.

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo tare da babban sakataren Majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres, a Hedikwatar Majalisar da ke birnin New York. 20 ga watan Yuli, 2018.
Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo tare da babban sakataren Majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres, a Hedikwatar Majalisar da ke birnin New York. 20 ga watan Yuli, 2018. REUTERS/Brendan McDermid
Talla

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo da jakadiyar kasar a Zauren majalisar dinkin duniya Nikki Haley sukai wannan kira, bayan gabatar da jawabi a zauren kwamitin tsaron majalisar.

Kiran da Amurka ta yin a cigaba da tsaurara takukumanm da aka kakabawa Korea ta Arewa, ya biyo bayan, kudirin da kasashen Rasha da China suka gabatar, na neman a tattauna kan yiwuwar dage takunkuman.

A makon da ya gabata ne Amurka ta gabatarwa zauren kwamitin Tsaro na majalisar dinkin duniya korafin cewa, duk da takunkuman hana saidawa Korea ta Arewa man fetur, daga farkon wannan shekara zuwa 30 ga watan Mayu, Korea ta Arewan ta yi fasakaurin man fetur cike a akalla manyan jiragen ruwa 89.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.