Nickolay Mladenov ya bukaci sasantawa tsakanin bangarorin biyu da nufin kaucewar bunkasuwar rikicin da ka iya juyewa zuwa wani salo daban.
Hamas ta sanar da cewa Israila ta yi amfani da jiragen sama da kuma tankunan yaki wajen kai farmaki yankin na Gaza, wanda nan ta ke ta hallaka Falasdinawa 4 bayan da ta yi luguden wuta kan jami'an da ke tsaron iyaka.
Ka zalika Ma’aikatar lafiya a yankin na Gaza ta sanar da cewa Isra'ilan ta kuma hallaka Bafalasdine na hudu ne yayin zanga-zangar da ta gudane inda ta harbe matashin har lahira.
Zanga-Zangar ta yau ita ce ta baya-bayan da Falasdinawan suka shafe watanni suna yi tun bayan ayyana kudus a matsayin babban birnin Israila, wanda ke barazana ga yiwuwar barkewar sabon yaki tsakanin Israilan da Hamas, Wadanda sukayi yaki har so uku cikin shekaru 10.
Sai dai a wata sanarwa da wani sojin Israila ya fitar, ta ce tun farko Falasdinawan ne suka fara harbe jami'ansu da ke tsaron kan Iyaka dalili kenan da ya tilasta musu daukar matakin ramuwa.