Bakonmu a Yau
Malam Umar Shitu Babura dokar da ke ayyana Isra'ila a matsayin kasar Yahudawa zalla
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:54
Majalisar dokokin Isra’ila ta amince da dokar da ke ayyana Isra’ila a matsayin kasar Yahudawa zalla. Manazarta dai na ganin cewa matakin, zai haifar da illa sosai ga yunkurin samar da kasar Palasdinu mai cikakken ‘yanci, yayin da sauran kabilu musamman larabawa da ke zaune a kasar za su iya fuskantar wariya.A zantawarsu da Abdoulkarim Ibrahim Shikal, Malam Umar Shitu Babura, masani siyasar kasashen yankin Gabas ta Tsakiya, ya bayyana yadda yake kallon wannan mataki na Isra’ila.