Saurare Saukewa Podcast
 • Labarai 06h00 - 06h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 24/03 06h00 GMT
 • 06h00 - 06h17 GMT
  Labarai 22/03 06h00 GMT
 • Shirye-shirye 06h06 - 06h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 24/03 06h06 GMT
 • 06h17 - 06h27 GMT
  Shirye-shirye 22/03 06h17 GMT
 • Labarai 07h00 - 07h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 24/03 07h00 GMT
 • 07h00 - 07h17 GMT
  Labarai 22/03 07h00 GMT
 • Shirye-shirye 07h06 - 07h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/03 07h06 GMT
 • 07h17 - 07h27 GMT
  Shirye-shirye 22/03 07h17 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/03 16h00 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h30 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 22/03 16h00 GMT
 • Shirye-shirye 16h06 - 16h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/03 16h06 GMT
 • Labaran Duniya 16h30 - 16h40 GMT Litinin-Jumma`a
  Labarai 22/03 16h30 GMT
 • Labarai 16h00 - 16h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/03 16h30 GMT
 • Shirye-shirye 16h36 - 16h56 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/03 16h36 GMT
 • Ra'ayoyin Masu Saurare 16h40 - 16h55 GMT Litinin-Jumma`a
  Jin Ra'ayoyin Masu Saurare 22/03 16h40 GMT
 • 20h00 - 20h17 GMT
  Labarai 22/03 20h00 GMT
 • Labarai 20h00 - 20h06 GMT Asabar-Lahadi
  Labarai 23/03 20h00 GMT
 • Shirye-shirye 20h06 - 20h26 GMT Asabar-Lahadi
  Shirye-shirye 23/03 20h06 GMT
 • 20h17 - 20h27 GMT
  Shirye-shirye 22/03 20h17 GMT
Domin more wa abubuwan da ke ciki, dole ne a tabbatar da cewa an sanya Flash Domin shiga sai an hada cookies a cikin shafin bincike
Duniya

Rikicin makiyaya na ta'azzara a Najeriya - MDD

media Rikicin manoma da makiyaya ya lakume rayuka da dama a Najeriya REUTERS

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, rikicin manoma da makiyaya na ci gaba da ta’azzara da kuma haddasa asarar rayuka masu yawa a tarayyar Najeriya, yayin da ta bukaci kara kaimi wajen magance matsalar Boko Haram.

Manzon musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Yammacin Afrika da kuma yankin Sahel, Mohamed Ibn Chambers ya shaida wa Kwamitin Sulhu na Majalisar cewa, rikicin manoma da makiyaya na matsayin babban kalubalen tsaro a yankin, tare da gargadin cewa, matsalar ka iya rikidewa zuwa ga hare-haren ‘yan ta’adda.

Chambers ya ce, a cikin kwanaki hudu na watan Yunin da ya gabata, sabbin hare-hare da kuma kashe-kashen daukan-fansa sun haddasa asarar dimbin rayuka musamman a yankin arewa ta tsakiya.

Jakadan ya ce, duk da nasarar yaki da Boko Haram a Najeriya, har yanzu mayakan na cin karansu babu babbaka a yankin tafkin Chadi domin kuwa, ba su daina amfani da mata da kananan yara wajen kaddamar hare-haren kunar bakin wake ba.

A cewarsa, hare-haren baya-bayan da aka kaddamar kan sojin Najeriya a Yobe da kuma konton-baunar da aka yi wa jerin gwanon motocinsu a Borno, na nuna cewa har yanzu Boko Haram na yin barazana.

Akwai dai bukatar kara kaimi ta fuskar diflomasiya da tsaro da kuma agajin jin-kai game da rikicin Boko Haram kamar yadda Ibn Chambers ya bayyana.

A game da wannan maudu'i
Sharhi
 
Yi hakuri lokacin ci gaba da kasancewa da mu ya kure