Isa ga babban shafi
Amurka-Birtaniya

Trump ya isa Birtaniya duk da boren 'yan kasar

Shugaban Amurka Donald Trump ya isa Birtaniya, in da ya ce, ya yi na’am da zanga-zangar da ake gudanarwa a yayin ziyararsa a kasar.

Shugaba Donald Trump na Amurka.
Shugaba Donald Trump na Amurka. REUTERS/Leah Millis
Talla

Shugaba Trump da mai dakinsa, Melania Trump sun isa birnin London a yammaci ranar Alhamis cikin jirgin sama na Air Force One kafin daga bisa a kwashe su a wani jirgi mai saukar ungulu zuwa gidan jakadan Amurka a Birtaniya.

Shugaba Trump zai gana da Firaministar Birtaniya, Theresa May wadda ke neman kulla yarjejeniyar kasuwanci bayan ficewar kasarta daga Kungiyar Tarayyar Turai, yayin da shugaban ya ce, kasar Birtaniya na cikin tsaka mai wuya.

An  jibge jami'an tsaro don sanya ido kan masu znga-zanga a yayin wannan ziyarar, yayin da Trump ya ce, yana zaton mutanen Birtaniya na matukar kaunarsa.

Rahotanni na cewa, ana zanga-zangar ce don nuna adawa da matakin Trump na kin karbar baki.

Trump wanda zai gana da Sarauniyar Ingila a yayin ziyarasa ta kwanaki biyu, ya ce, yana ganin Birtaniya ta zabi ficewa daga Tarayyar Turai ne saboda batun shige da fice.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.