Isa ga babban shafi
Amurka-NATO

An samu gagarumar nasara a NATO-Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana samun gagarumar nasara wajen matasa wa kasashen da ke cikin Kungiyar Kawancen Tsaro ta NATO wajen kara kudin da suke zubawa cikin asusun kungiyar.

Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump REUTERS/Yves Herman
Talla

Sai dai a gefe daya shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce maganar ta shugaban na Amurka nada gyara, domin kuwa babu wani sauyi da aka samu kan kudin da suke biya.

Shugaba Trump ya yi ikirarin samun nasarar ce bayan caccakar kawayen Amurka musamman Jamus kan yadda suka gaza biyan kudaden samar da tsaro a yayin wani taro da ake kallo a matsayin mafi zafi da suka gudanar cikin shekaru 70.

Mr. Trump ya sabbaba gudanar da wani zaman gaggawa kan batun kashe kudaden, yayin da ya wanke kansa daga rahoton da ke cewa, ya yi barazanar ficewa daga NATO, in da ya ce, ya yi amanna da wannan kungiya.

Mr. Trump ya haifar da tayar da jijiyoyin wuya ne a taron na ranar Laraba, bayan ya bukaci sauran kasashen NATO da su kara kudaden da suke kashewa da kashi biyu a ma’aunin karfin tattalin arziki na GDP a maimakon  jinkirta karin har zuwa shekarar 2024 kamar yadda suka amince a can baya.

Daga bisani Trump ya kara ruda tunanin kasashen bayan ya ce mu su, su rubanya kudaden zuwa kashi hudu.

Sai dai shugaba Macron ya musanta ikirarin Trump, in da ya ce, yarjejeniyar da suka sanya wa hannu ta tsaya ne kan abin da suka amince da shi a can baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.