Isa ga babban shafi
Afrika

MDD da AU za su hada kai don magance rikicin Afrika

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da shugaban gudanarwar Kungiyar Kasashen Afrika Musa Faki Muhammad, sun bukaci hadin kan hukumomin biyu domin shawo kan tashe-tashen hankulan da ake samu a nahiyar Afrika.

Shugaban gudanarwar Kungiyar Kasashen Afrika, Moussa Faki
Shugaban gudanarwar Kungiyar Kasashen Afrika, Moussa Faki Flickr/CC/Chatham House/©Suzanne Plunkett 2017
Talla

A wani taro da suka saba gudanarwa duk shekara, shugabannin biyu sun mayar da hankali kan yadda za a rika magance rikice-rikicen da ake samu ta hanyar nazarin abin da ke haddasa su da kuma karfafa matakan siyasa da mutunta bangaren shari’a.

Taron ya kuma duba kalubalen tsaro da zaman lafiyar da ake fsukanta a kasashen Burundi da Janhuriyar Afrika ta Tsakiya da Yankin Tafkin Chadi da Comoros da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da Madagascar da Mali da Somalia da kuma Sudan ta Kudu, in da shugabannin suka amince su kara yawan goyan bayan da suke bayarwa domin tabbatar da zaman lafiya.

Shugaban Kungiyar Kasashen na Afrika, ya yi wa  Guterres bayani kan matsayin taron shugabannin Afrika da aka gudanar a baya-bayan nan, yayin da kuma ya ba shi karin haske rikicin yammacin Sahara da na kasar Libya da kuma farfado da gidauniyar zaman lafiya ta kasashen Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.