Isa ga babban shafi
Turkiya

Erdogan ya sake lashe zaben Turkiya

Hukumar Zabe a kasar Turkiya ta bayyana shugaba Recep Tayyip Erdogan a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar, matakin da zai tsawaita mulkinsa na shekaru 15.

Shugaba Recep Tayyip Erdogan a gaban dimbin magoya bayansa da suka jefa masa kuri'a a Turkiya
Shugaba Recep Tayyip Erdogan a gaban dimbin magoya bayansa da suka jefa masa kuri'a a Turkiya REUTERS/Umit Bektas
Talla

Shugaban Hukumar zaben kasar, Sadi Guven ya ce kashi 88 na masu rajistar zabe ne suka kada kuri’a, yayin da shugaba Erdogan ya lashe sama da kashi 53, sai kuma Muharrem Ince da ya zo na biyu da kashi 31.

Tuni aka fara bukukuwa a gidan shugaban da kuma ofishin Jam’iyyarsa ta AKP da ke birnin Ankara, yayin da abokin takararsa Ince ya ce, nan gaba kadan zai bayyana matsayinsa dangane da sakamakon zaben.

Yayin da yake jawabi a gaban daruruwan magoya bayansa, shugaba Erdogan ya ce, al’ummar kasar sun sake dora masa nauyin tafiyar da kasar, kuma ya sha alwashin gaggauta aiwatar da sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Zababben shugaban ya ce, Turkiya ta bai wa sauran kasashen duniya darasi kan yadda ake gudanar da dimokiradiya.

Tuni shugabannin kasashen duniya suka fara aika masa da sakon taya murna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.