Isa ga babban shafi
China-Faransa

China ta janye Faransa takunkumi kan naman shanu

Firaministan Faransa, Edouard Phillippe ya kammala ziyarar kwanaki 4 da ya kai kasar china wadda kuma ita ce irinta ta farko tun bayan fara mulkinsa inda ya gana da manyan kamfanonin kasar ta China.Phillippe ya sanya hannu kan fiye da yarjeniyoyi 10 galibi wadanda suka shafi kirkire-kirkiren Fasaha da Noma da kuma Muhalli gabanin barowar ta sa China a yau Litinin. 

Za a iya kwatanta ziyarar ta Firaminista Edouard Philippe a matsayin mafi tasiri da wani shugaban Faransa ya taba kai wa China..
Za a iya kwatanta ziyarar ta Firaminista Edouard Philippe a matsayin mafi tasiri da wani shugaban Faransa ya taba kai wa China.. Reuters
Talla

Yayin ziyarar ta Edourad Phillippe ya yi gagarumar nasarar kawo karshen takunkuman da China ta sanya kan Naman shanun Faransa fiye da shekaru 17 da suka gabata bayan wata annobar cutar shanu da Faransar ta fuskanta.

Haka zalika Firaminstan na Faransa ya tattauna da mahukuntan kasar ta China game da batutuwan da suka shafi kare sirrin jama'a ta yanar intanet, yaki da gurbacewar yanayi, dama samar da daidaito ta fuskar kasuwanci.

Firaminista Philippe ya ce babu ta yadda za a samu ingantacen ci gaba mai dorewa ba tare da bin kaídodi ba, batare kuma da aiki da kaídojin gaskiya a tsarin bai daya na duniya ba, ba kuma tare da yakar rashin gaskiya da kuma tabbatar da adalci ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.