Isa ga babban shafi
Faransa

An cafke maharan da suka shirya far wa Musulmin Faransa

Jami’an Rundunar Yaki da Ayyukan Ta’addanci a Faransa, sun cafke mutane 10 da ake zargin cewa sun shirya kai hari a kan Musulimin kasar, in da tuni aka danka lamarin a hannun ma’aikatar shari’a domin gudanar da bincike.

Jami'an tsaron Faransa sun cafke wasu mutane 10 da ke shirin kai hari kan Musulman Faransa
Jami'an tsaron Faransa sun cafke wasu mutane 10 da ke shirin kai hari kan Musulman Faransa AFP
Talla

Masu bincike na ma’aikatar shara’ar Faransa sun ce kafin cafke su, tuni mutanen 10 suka yi nisa wajen tsara kai munanan hare-hare a kan Musulmin kasar.

Hukumar Tara Bayanan Sirrin ce, wato DGSI ta bankado wannan yunkuri, in da nan take ta sanar da sashen yaki da ayyukan ta’addanci na rundunar ‘yan sanda, wanda ya dauki matakan gaggawa domin cafke mutanen.

Binciken farko ya tabbatar cewa wadanda ake zargin, tuni suka fara sayo makaman da za su yi amfani da su domin afka wa Musulmin, makaman da majiyar tsaron ta ce an gano in da aka tara su bayan tatsar bayanai daga masu shirin kai harin.

Biyu daga cikin mutanen an cafke su ne a garin Ajaccio na yankin Corse a ranar Asabar da ta gabata, kuma ga alama mutanen na da alaka da kungiyoyin masu zazzafan ra’ayi, wariyar jinsi da kuma kyamar baki a cikin kasar ta Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.