Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya janye shirin raba 'ya'yan 'yan cirani da iyayensu

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu kan kudirin da ke dakatar da shirin raba yara kanana iyayensu da suka shiga kasar ba a kan ka’ida ba, sakamakon sukar da shirin ya fuskanta a ciki da wajen kasar ta Amurka.

Donald Trump Shugaban Amurka.
Donald Trump Shugaban Amurka. REUTERS/Leah Millis
Talla

Shugaban na Amurka Donald Trump ya dau wannan mataki ne a ofishin sa da ke fadar gwamnatin kasar ta White House.

Trump dai ya fuskanci suka daga kasashe, kungiyoyin kare hakkin bil Adam mambobin majalisar kasar dama uwa uba iyalan shi da suka kunshi matarshi da ‘Yarsa Ivanka.

Uwargidan Donald Trump Ivanka Trump ta yi kakkausar suka inda ta ce bai dace a raba kananan yara da iyayensu ba.

Shugaba Trump ya ce Amurka za ta dauki matakin ganin iyalan ‘yan ci ranin sun ci gaba da kasancewa a hade, don haka zai sanya hannu kan dokar ne domin basu kariya kan shirin na sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.