Isa ga babban shafi
Amurka- 'Yan cirani

Trump zai janye shirinsa na raba yaran 'yan cirani da iyayensu

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da aniyarsa ta sanya hannu kan wata doka da za ta kawo karshen shirinsa na raba ‘ya’yan ‘yan ciranin da suka shigo kasar ba bisa ka’ida ba da iyayensu bayan fuskantar kakkausar suka hatta daga iyalansa.

Shugaban Amurka Donald Trump lokacin da yake kokarinsa sanya hannu kan dokar da za ta bayar da kariya ga 'yan ciranin da suka shiga kasar ba bisa ka'ida ba yau laraba a Ofishinsa da ke fadar gwamnatin kasar ta White House.
Shugaban Amurka Donald Trump lokacin da yake kokarinsa sanya hannu kan dokar da za ta bayar da kariya ga 'yan ciranin da suka shiga kasar ba bisa ka'ida ba yau laraba a Ofishinsa da ke fadar gwamnatin kasar ta White House. REUTERS/Leah Millis
Talla

Shugaban na Amurka Donald Trump wanda ke wannan batu a ofishinsa da ke fadar gwamnatin kasar ta White House ya ce zai sanya hannu kan dokar kowanne lokaci a yau Laraba.

A gobe Alhamis ne kuma majalisar kasar za ta yi zama na musamman kan dokar ta shugaba Trump.

Trump dai ya fuskanci suka daga kasashe kungiyoyin kare hakkin dan adam mambobin majalisar kasar dama uwa uba iyalanshi da suka kunshi matarshi da ‘Yarsa Ivanka.

Ko a dazu da safe Ivanka Trump ta yi kakkausar suka kan matakin mahaifin na ta inda ta ce bai dace a raba kananan yara da iyayensu ba.

A cewar Trump Amurka za ta dauki matakin ganin iyalan ‘yan ci ranin sun ci gaba da kasancewa a hade, a don haka zai sanya hannu kan dokar da za ta basu kariya kan shirin na sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.